Home » Mataimakiyar Shugaban Ƙasar Amurka Ta Yaba Wa Shugabar Ƙasar Tanzania

Mataimakiyar Shugaban Ƙasar Amurka Ta Yaba Wa Shugabar Ƙasar Tanzania

by Anas Dansalma
0 comment

Mataimakiyar shugaban ƙasar Amurka Kamala Harris ta yaba wa Tanzaniya kan sauye-sauyen da ta kawo wanda ke da zimmar ƙarfafa dimokuraɗiyyar ƙasar.

Harris na a Tanzaniya a ci gaba da ziyara da take yi a Afirka bayan farawa Ghana, inda za ta kammala ziyarar a karshen mako da ƙasar Zambia.

An yi wa KAMALA Harris kyakkaywar tarba ta hanyar rera wakoki da yin rawan al’adu daban-daban.Shugabar ƙasar ta Tanzaniya, Samia Suluhu Hassan, ta kwatanta ziyarar da wani babban ci gaba ga ƙasar.

Harris ta ce Amurka za ta bai wa Tanzaniya tallafin $560m don buƙasa kasuwancinta da kuma karfafa dimokuraɗiyya.Abu ne da ba a saba gani ba na ziyarar wani babban jami’in gwamnatin Amurka zuwa ƙasar, inda wasu da dama ke ganin ziyarar a matsayin nuna goyon baya ne ga sauye-sauye da Samia ke yi.

Tun bayan karɓe iko da mulkin ƙasar bayan mutuwar shugaba John Magufuli shekara biyu da suka gabata, Samia ta ɗage haramci kan yakin neman zaɓen ƴan adawa da kuma karfafa ƴancin ƴan jarida. Ƴan siyasa da suka tafi neman mafaka duka sun dawo gida.

Ms Harris ta yaba da matakan da ƙasar ke ɗauka na kawosauye-sauye, inda ta ce hakan ya taimaka wajen kara kyautata dangantakar ƙasashen biyu.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi