Mataimakiyar shugabar Amurka, Kamala Harris ta samu tarba daga ‘yan makaranta da masu kade-kade da raye-raye na gargajiya, a lokacin da ta isa filin tashi da saukar jiragen sama na Kotoka na kasar Ghana.
Mataimakiyar shugabar Amurka, ta yi jawabi jim kadan bayan saukarta a filin tashi da saukar jiragen sama na Kotoka, da ke Accra, in da mika gaisuwar shugaban kasa da daukacin al’ummar Amurka tare da fatan wannan tafiya za ta kara kyakkyawar alaka da abota tsakanin al’ummar Amurka da mazauna nahiyar Afirka.
Ta bayyana kudurinta na tattaunawa da za ta samar da damarmaki a sassa daban-daban na nahiyar da za su amfani al’ummar nahiyar da ma duniya baki daya.
A cewar Kamala, ganawa da za ta yi da Shugaban Ghana da da na Tanzaniya da Zambiya, za su dora daga inda suka tsaya a tattaunawa da su ka fara a taron Afirka da aka gudanar a Amurka watannin baya, kan karfafa dimokradiyya da shugabanci na gari, da samar da zaman lafiya da tsaro, da bunkasar tattalin arziki mai dorewa, da karfafa huldar kasuwanci.
Mataimakin shugaban kasar Ghana, Dakta Mahamudu Bawumia ne ya jagoranci jami’un gwamnati da suka tarbe ta, kewaye da masu kide-kide da raye-rayen gargajiya da ‘yan makaranta suna daga tutocin Ghana da na Amurka.