Kungiyar ‘Yan Kasuwa, Masana’antu, Ma’adanai, da Noma ta Kano, KACCIMA, ta ce tana shirin sanyawa cibiyar kasuwanci da taro da sunan Shugaban Kamfanin Dangote Group, Aliko Dangote.

Matatar Man Dangote Ta Rage Farashin Fetur Zuwa N699

Matatar man Dangote ta sake rage farashin man fetur ɗin da take sayar da man, inda ta rage farashin man fetur ɗin daga Naira 828 zuwa Naira 699 kan kowace lita.

Bayanan farashin da aka wallafa a shafin  kasuwancin farashin man fetur a Petroleumprice.ng a ranar Juma’a sun nuna cewa matatar ta aiwatar da wani bita na baya-bayan nan, inda ta rage farashin man da N129 a kowace lita – ragin kashi 15.58 cikin 100.

Wani jami’in matatar man da ya zanta da manema labarai bisa sharaɗin sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin tsokaci a bainar jama’a, shi ma ya tabbatar da yin ragin.

Ya ce, matatar man ta rage farashin man fetur zuwa N699 kowace lita.

Sabon farashin ya fara aiki ne daga ranar 11 ga watan Disamba, 2025, wanda ya yi daidai da farashin man fetur karo na 20 da matatar man ta sanar a bana.

Ragi na baya-bayan nan ya zo ne kwanaki biyar bayan shugaban matatar, Aliko Dangote ya jaddada ƙudirinsa na ganin an tabbatar da farashin man fetur a cikin gida cikin “madaidaicin farashi a kasuwanni” duk kuwa da taɓarɓarewar da ake samu a duniya da fasaƙwaurin da ake yi a kan iyakokin Najeriya.

Da yake bayani bayan ganawar sirri da shugaban Najeriya, Bola Tinubu a ranar 6 ga watan Disamba, Dangote ya ce farashin zai ci gaba da faɗuwa yayin da matatar man ke ƙara yawan kayan da ake fitarwa da kuma yin gogayya kai tsaye da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *