Sojoji Sun Kashe ’Yan Bindiga 3 A Binuwai

Dakarun Sojin Operation Whirl Stroke (OPWS), sun kashe wasu mutum uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, yayin wani samame da suka kai a Ƙaramar Hukumar Ukum, a Jihar Binuwai.

Mai magana da yawun OPWS, Laftanar Ahmad Zubairu, ya ce sojojin sun samu bayanan sirri kuma suka yi aiki tare da ’yan sandan Zaki-Biam.

Maharan sun kafa shinge a kan hanyar Aturuku–Wembe–Ayati, inda suke tare matafiya suna ƙwace musu kayayyaki.

Da sojoji suka isa wajen, maharan sai suka fara harbe-harbe, wanda hakan ya sa sojojin suka buɗe musu wuta.

Hakan ya yi sanadin mutuwar uku daga cikinsu, sauran kuma suka tsere cikin daji.

Dakarun sun ƙwato babura guda biyu, yayin da suka ci gaba da farautar waɗanda suka tsere.

Bincike ya nuna cewa mutanen da suka mutu suna cikin wata ƙungiya da ta daɗe tana yi wa al’umma barazana ta hanyar garkuwa da mutane da kai hare-hare, musamman kusa da kasuwar doyar Zaki-Biam.

Mutanen gari sun tabbatar da sunan waɗanda dakarun suka kashe.

Kwamandan OPWS, Manjo-Janar Moses Gara, ya yaba wa sojojin bisa ƙwazo da jarumtarsu, tare da alƙawarin ci gaba da kare al’umma da tabbatar da zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *