Hukumar karɓar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar kano karkashin jagorancin Barr. Muhuyi Magaji Rimin Gado ta kwato wasu motocin kwashe shara guda goma 12 mallakin gwamnatin jiha.
Idan za’a iya tunawa bayan mayar da Muhuyi Magaji kan mukaminsa ya sha alwashin zai yi aiki ba sani ba sabo wajen ganin an kwato wa mai hakki hakinsa.
Motocin dai a yanzu suna cikin harabar hukumar karɓar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar kano mallaki ne ga hukumar kwashe shara ta jihar kano.
Yayin da ya ziyarci hukumar domin ganewa idanunsa motocin da aka kwato, kwamishinan harkokin Sufuri da gidaje na jihar kano, Engr. Muhammad Diggwal yace motocin an rasa su ne tun a gwamnatin data gabata, wanda hakan tasa gwamnan kano Abba Kabir Yusuf ya ba da
Engr. Muhammad Diggwal yace zasu jira hukumar ta kammala bincike a kan yadda aka motocin suka bace, ya yake da alhakin batan nasu, sanann sai hukumar ta ɗauki matakin da ya dace akan Wanda aka samu da laifi, Kuma a basu motocin don su cigaba da amfanar al’ummar jihar kano.