Home » Mun Bar Kundi Ga Sabuwar Gwamnati Kan Cire Tallafin Mai – Boss Mustapha

Mun Bar Kundi Ga Sabuwar Gwamnati Kan Cire Tallafin Mai – Boss Mustapha

by Anas Dansalma
0 comment
Muna da Ƙarfin Gwuiwa Game da Sabuwar Gwamnati Kan Cire Tallafin Mai - Boss Mustapha

Gwamnatin Najeriya ta ce ta tsara wani kundi da zai taimakawa sabuwar gwamnati ta Bola Tinubu, kan yadda za ta cire tallafin mai ba tare da wata matsala ba.

Gwamnatin Buhari ta sanar da cewa ta yi iya kokarinta wajen ganin ta tafiyar da harkokin tallafin mai, da har ya kai gwamnati kashe naira tiriliyan 13 daga shekarar 2005 zuwa 2021.

Sakataren gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya ce daga cikin abubuwan da ake tattauna game da cire tallafin man fetur ɗin, shi ne bukatar gyaran matatun man kasar da samar da shirin da zai rage wa mutane radadi tasirin janye tallafin musamman ga talakawa da ma’aikata.

A ranar 29 ga watan Mayu ake saran rantsar da Bola Tinubu a Abuja.

Majiyarmu ta rawaito Boss Mustapha na cewa yana jadadda ƙwarin gwuiwarsa game da sabuwar gwamnati da za a rantsar kan za ta gudanar da ayyuka da yanke hukunci ba tare da cutar da al’umma ko jefa mutane cikin matsi ba.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi