Wata matashiya a jihar Legas ta kafa tarihi na zama wadda ta fi daukar lokaci mai tsawo tana girki a duniya ba tare da tsayawa ba.
Ya zuwa safiyar wannan rana ta Litinin da misalin karfe 08:32 na safe, Hilda Bassey, wacce aka fi sani da Hilda Baci, ta shafe awanni 88 da minti 32 tana girki.
Hilda, mai sana’ar girki a Jihar Legas da ke kudancin ƙasar nan, ta doke takwararta ‘yar India Lata Tondon wadda ta shafe sa’o’i 87 da mintuna 45 tana girki a babu tsayawa a shekarar 2019.
A wata hira da ta yi da ‘yan jarida, Hilda ta bayyana cewa tun tuni ta saka a ranta cewa za ta yi wannan girkin bayan da ta ga Lata ta yi makamancinsa.
Baci, mai shekara 27, ta soma wannan girki ne a ranar 11 ga watan Mayu wanda batun girkin nata ya mamaye shafukan sada zumunta musamman a Nijeriya da kuma Afirka inda aka yi ta karfafa mata gwiwa.
Cikin waɗanda suka ƙarfafa mata guiwa har da gwamnan Legas Baba Jide Sanwo-Olu wannda ya yi takakki har wurin da take girkin, inda ya ba ta kwarin gwuiwa da kuma murnar cewa ana gudanar da wannan babban abu a cikin jiharsa.