Wani jirgin sama mallakin kamfanin sufuri na Air Indiya ya yi hatsari inda ya faɗa kan wata unguwa da ke birnin Ahmedabad a yammacin ƙasar Indiya.
Ana da yaƙinin cewa akwai aƙalla fasinjoji da ma’aikata 240 a cikin jirgin.
Bidiyo da ake yadawa a shafukan sada zumunta ya nuna baƙin hayaƙi ya turnuƙe bayan rikitowar jirgin.
Babu tabbacin adadin mutanen da suka mutu ko suka jikkata sanadiyyar hatsarin, amma da iwasu rahotanni na cewa akalla mutane 40 suka rasa rayukansu kamar yadda PMNEWS ta wallafa.
Jirgin na kan hanyarsa ne daga Indiya zuwa Birtaniya.
Akwai Indiyawa 169 a jirgin da ƴan Birtaniya 53, da ɗan ƙasar Canada ɗaya sai kuma ƴan ƙasar Portugal guda bakwai, kamar yadda kamfanin sufurin ya bayyana.
Ma’aikatan kashe gobara da masu bayar da agajin gaggawa sun garzaya wurin da lamarin ya faru.

