• Home  
  • Masu Zanga-Zanga Sun Fito A Biranen Najeriya
- Babban Labari - Labarai

Masu Zanga-Zanga Sun Fito A Biranen Najeriya

Masu zanga-zanga sun fito a biranen Najeriya domin kokawa kan halin da ƙasar ke ciki yayin da ƙasar ke bikin ranar dimkuraɗiyya a yau Alhamis. A birnin Ibadan na jihar Osun masu zanga-zangar na ɗauke ne da allunan waɗanda suka ƙunshi saƙo daban-daban. Daga cikin abin da masu zanga-zangar ke kokawa a kai akwai talauci […]

Masu zanga-zanga sun fito a biranen Najeriya domin kokawa kan halin da ƙasar ke ciki yayin da ƙasar ke bikin ranar dimkuraɗiyya a yau Alhamis.

A birnin Ibadan na jihar Osun masu zanga-zangar na ɗauke ne da allunan waɗanda suka ƙunshi saƙo daban-daban.

Daga cikin abin da masu zanga-zangar ke kokawa a kai akwai talauci da matsin rayuwa, waɗanda suke zargin manufofin gwamnati sun haifar.

Cire tallafin man fetur da sauye-sauye a ɓangaren kudi sun haifar da tashin farashin kayan masarufi da zubewar darajar kudin ƙasar, kamar yadda masana suka bayyana.

Sai dai gwamnatin ƙasar ta ce manufofin nata za su amfani a ƙasar a nan gaba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000