Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya bayyana cewa shugaba Tinubu mutun ne mai tawali’u da ƙanƙan da kai kuma bai yarda da al’mubazzaranci ba.
A cewar wata majiya, Shettima ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a wani taron ƙaddamar da littafi a Abuja. Ya ƙara da cewa gidansa na Maiduguri ya fi gidan Tinubu na Legas.
“Tinubu shugaba ne da za mu iya bai wa yardarmu , ba maganar siyasa nake yi ba, yana nufin mutanen Najeriya da alheri, ba kuma ya zo mulki ba ne don ya tara abin duniya.” a cewar Shettima.
Na fi shugaba Tinubu saka kaya masu tsada, tun da na hadu da shi agogonsa daya yake amfani da shi.” – Kashim Shettima.
71