Yar takarar kujerar gwaman jihar Adamawa ƙarƙashin jam’iyyar APC Sanata Aishatu Ahmed Binani, ta bayyana goyon bayanta kan matakin da hukumar zaɓen ƙasar INEC ta ɗauka na bayyana zaɓen gwaman jihar a matsayin wanda bai kammala ba.
Babban jami’in tattara sakamakon zaɓen jihar Farfesa Muhammadu Mele na jami’ar Maiduguri ne ya ayyana sakamakon zaɓen gwaman jihar da a ka gudanar a ranar 18 ga watan Maris a matsayin wanda bai kammala ba.
Gwaman jihar mai ci Ahmadu Umaru Fintiri, wanda ke neman wa’adin mulkin jihar karo na biyu ƙarƙashin jam’iyyar PDP ya samu ƙuri’u 421,524, yayin da ita kuma Sanata Binani ta jam’iyyar APC ke da yawan ƙuri’u 390,275.
Jami’in zaɓen ya bayyana cewa ba a gudanar da zaɓen a rumfunan zaɓe 69 a faɗin jihar ba, kuma adadin katunan zaɓen da aka karɓa a duka rumfunan sun kai 37,016, wanda kuma adadinsu ya zarta tazarar ƙuri’u 31,249 da ke tsakanin ‘yan takarar biyu. Sanata Aisha ta bayyana cewa a ra’ayinta matakin da jami’in tattara sakamakon zaɓen jiha ya yi daidai ne bayan bayyana sakamakon zaɓen jihar a matsayin wanda bai kammala ba.