Tsohon gwamnan jihar Sakkwato Attahiru Bafarwa da kuma fitacciyar ‘ƴar gwagwarmaya a Arewacin Najeriya, Hajiya Naja’atu Muhammad, sun ƙaddamar da wata sabuwar tafiyar matasa don ceto yankin Arewacin Najeriya me suna Northern Star Youth Movement Initiative (NSYMI).
A jawabinsa, Bafarawa wanda tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ne a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ya ce, lokaci ya yi da matasa za su karɓi jagoranci. Idan aka basu dama, za su taka rawar gani, a cewar Bafarawa, ya kuma ƙara da cewa ƙungiyar na Shirin buɗe ofisoshi a faɗin ƙasar nan.
- Lamiɗo Ya Zama Sarkin Ƙananan Hukumomi 3 Maimakon 8
- Malaman Jami’ar legas Sun Koma Kwana A Ofis Saboda Tsadar Rayuwa
A ranar Talata ne manyan ƴan siyasar Arewan suka ƙaddamar da tafiyar matasan da nufin tallafawa matasa,da kuma ɓullo da hanyoyin magance matsalolin da suka dabaibaye yankin.
A nata ɓangaren, Hajiya Naja’atu Mohammed, ta jaddada cewa ƙungiyar ba ta siyasa ba ce, ta mayar da hankali ne kawai wajen tallafa wa matasa da kuma kawo cigaban yankin Arewacin Najeriya.
“Manufarmu a fili take, amfani da ƙarfi da kuma basirar da Allah Ya yi wa kowane ɗan Arewa domin kawo cigaban rayuwa da na tattalin arziki a yankin,” in ji Hajiya Naja’atu.
A watannin baya dai an kafa wata makamanciyar wannan tafiyar da aka kira da “The Youth Movement,” wato tafiyar matasa.