Daga Hauwa Sani Ibrahim
Ukashatu Lawan Diza wani mai laurar gani (makanta) ya bayyana mana cewa a yanzu halin da ake ciki a Najeriya masu bukata ta musamman sun fi sauran jama’a kamuwa da cutar damuwa.
A tattaunawar ta mu da Ukashatu ya bayyana mana cewa suna cikin wani hali mara daɗi, duba da tsangwama da rashin kula da kuma yadda ake nuna musu cewa su ba cikakkun mutane ba ne.
Ya ce, tsangwama da rashin kula na taka rawar gani wajen haifar musu da cutar damuwa wato “Depression” da Turanci.
- Naja’atu da Bafarawa Sun kafa Sabuwar Tafiyar Matasa
- Malaman Jami’ar legas Sun Koma Kwana A Ofis Saboda Tsadar Rayuwa
Ukashatu ya kara da cewa mafi yawan lokaci wadanda ke zagaye da masu bukata ta musamman na daga cikin waɗanda ke bada gudunmuwa wajen jefa su cikin halin da ke jawo musu kamuwa da cutar damuwa.
kuma babban abin tashin hankali ma shi ne rashin ɗaukar cutar damuwar tasu da muhimmanci sai ma a alaƙanta lamarin da taɓin hankalin ko shafar aljanu.
A karshe Ukashatu ya yi kira ga al’umma da gwamnati, su karfafa wa masu buƙata ta musamman tare da jan su a jika, sannan a ilimantar da su, domin kada su fada cikin wannan hali na kamuwa da cutar damuwa.