Hukumar yaƙi da hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA, reshen jihar Kano, ta ƙone haramtattun ƙwayoyi fiye da kilo dubu goma sha biyu.Kwamandan hukumar na jihar Kano, Dahiru Lawan Yahya, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar ƙone miyagun ƙwayoyin, a yankin hawan Kalebawa dake ƙaramar hukumar Dawakin-Tofa Kano.
Kwamandan NDLEA na Kano, CN Dahiru Yahaya Lawal, ya ce wannan mataki wani ɓangare ne na yaƙin da hukumar ke yi da shaye-shaye da fataucin miyagun ƙwayoyi, tare da jaddada cewa za ta ci gaba da bibiyar masu aikata irin waɗannan laifuka.
Hukumar ta ce tun daga farkon shekarar 2026 ta kama mutane fiye da 900 da ake zargi da hannu a harkar miyagun ƙwayoyi, yayin da kotuna suka yanke wa sama da mutum 50 hukunci.
NDLEA ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro, shugabannin addini da na gargajiya, makarantu da iyaye su haɗa kai wajen kare matasa daga shaye-shaye.
A nasa jawabin, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa NDLEA wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi, tare da haɗa matakan gyaran hali da dawo da matasa cikin al’umma.
