Miyagun kwayoyi: NDLEA ta kama mutum 80 a Kano
A mako guda, Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama mutum 80 tare da watsa maboya 16 na masu ta’ammali da miyagun kwayoyi a Jihar Kano. Hukumar ta fara samamen, mai suna “Operation Restore Order” ne daga ranar 10 zuwa 16 ga watan nan na Agusta, inda ta kai farmaki […]










