Sojojin rundunar Operation Hadin Kai sun ce sun ceto ɗalibai da malamai 10 da ƴan ƙungiyar ISWAP suka sace a wani hari da suka kai yankin Lassa da ke ƙaramar hukumar Askira/Uba a jihar Borno.
A wata sanarwa da mukaddashin jami’in yaɗa labarai na rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe tara na safiyar ranar Litinin, lokacin da mayaƙan suka kai hari makarantar sakandaren fasaha ta Lassa, inda ɗaliban ke rubuta jarabawar kammala sakandare NECO.
Sanarwar ta ce nan take rundunar ta tura sojoji tare da jiragen yaƙi domin gudanar da aikin ceto kuma bayan fafatawa da mayaƙan a yankin Daggu, sojojin sun samu nasarar ceto mutum 10 ba tare da sun ji rauni ba.
“Har yanzu ana ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran mutanen da suka rage, tare da kamo waɗanda suka aikata harin domin gurfanar da su a gaban shari’a,” in ji sanarwar.
Rundunar ta ce yayin artabun, sojojin sun kashe wasu daga cikin mayaƙan tare da ƙwace babura bakwai da suka yi amfani da su wajen kai harin, lamarin da ya hana su tserewa cikin sauƙi.
Sai dai rundunar ta ce an kashe wani soja da kuma mutum ɗaya daga cikin jami’an sa kai na JTF, a yayin musayar wuta da mayaƙan.
Duk da wannan nasara da rundunar sojin Najeriyar ta samu, har yanzu akwai ɗalibai sama da 50 da ke hannun ƴan bindigar da suka sace su a jihohin Borno da Oyo tun a watan Mayun 2026, inda gwamnatin ƙasar ta ce tana ci gaba da ƙoƙarin ceto su.
