Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa wato NEMA ta kai tallafi ga kauyuka biyu da suka gamu da annobar gobara a karamar hukumar kiyawa dage Jahar jigawa
Shugaban hukumar ta NEMA Mustafa Habib ya ce sun kawo kayan tallafi ne bisa umarnin ministar ba da tallafin jinkai Sadiyar Umar Faruk bisa sahalewar shugaban kasa muhammau Buhari .
Da yake amsar kayan tallafin, mataimakin gwamnan Jahar ta jigawa Umar Namadi,ya yaba wa shugaban hukumar da ta ba da agajin gaggawa da kuma ministar ba da tallafin jinkai da kuma uwa uba shugaban kasa Muhammad Buhari.
Idan dai za iya tunawa a ranar Alhamis din da ta gabata ne dai wata gobara da ta tashi a kauyukan malamawa da karangiya dake karamar hukumar kiyawa ta Jahar jigawa wacce ta yi sanadiyar kona dukiyoyi da dama.
Ko da a nan Jihar Kano an samu makamanciyar irin wannan gobara a kasuwar Rimi da ke nan Kano waɗana ake sa ran su ma tuni sun samu makamanciyar wannan tallafi.