Hukumar kula da wutar lantarki ta ƙasa NERC, ta hana kamfanonin rarraba wuta wato DisCos, karɓar kuɗaɗe daga hannun kwastomomin da aka yankewa wuta.
Ana sa ran wannan sabuwar doka za ta kare kwastomomin da ake amsar kuɗaɗen wuta fiye da ƙima daga hannun mutane. Dokar ta kuma zo da sabbin sharuɗa ga ma’aikatan kan yadda za su riƙa saurare da kuma kula da korafe-korafen kwastomominsu.
Haramcin na ƙunshe ne a wata takarda da shugaban hukumar ta NERC, Sanusi Garba ya sanyawa hannu kamar yadda Jaridar The Nation ta wallafa a shafinta.