Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ayyana neman tsohowar ministar jin ƙai ta ƙasar, Sadiya Umar Farouq ruwa a jallo.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na internet, ta ce tana neman tsohuwar ministar bisa zarge-zargen laifukan haɗa baki domin aikata laifuka da amfani da ofishi ba bisa ƙa’ida ba da karkatar da kuɗin gwamnati.
Sanarwar EFCCn ta buƙaci jama’a su sanar da hukumar duk inda suka ga tsohuwar ministan domin kama ta.
Sadiya Umar Farouq ta kasance tsohuwar ministar jin ƙai zamanin gwamnatin tsohon shugaban ƙasar, marigayi Muhammadu Buhari
