Tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya Super Eagles ta doke tawagar ƙasar Gabon a wasan neman tikitin shiga Gasar Kofin Duniya ta 2026 da suka fafata a yammacin wannan Alhamis.
Wasan wanda aka soma da ƙarfe 5 na yamma a filin wasa na Prince Moulay Hassan da ke Rabat a Morocco, ya bai wa Super Eagles damar lallasa The Panthers har ci 4-1.
Wannan sakamakon ya bai wa Nijeriya nasarar kaiwa zagayen ƙarshe a wasan cike gurbin shiga gasar Kofin Duniya na 2026.
Akor Adams ne ya fara ci wa Super Eagles ƙwallo a minti na 78, amma daga baya Gabon ta farke ta hannun Mario Lemina daf a tashi daga fafatawar.
A haka dai aka tashi 1-1 bayan minti 90 da suka buga, lamarin da ya sa aka yi ƙarin minti 30 saboda dole sai an samu wanda zai yi nasara.
- Majalisar Wakilan Najeriya Ta Nemi A Dage Soma Amfani Da Kwamfuta A Jarrabawar WAEC
- Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Satar Mota A Gidan Gwamnatin Kano
Bayan an dawo daga hutun ƙarin lokacin ne aka ci gaba da fafatawar har ta kai ga Super Eagles ta ƙara na biyu ta hannun Chidera Ejuke, sannan Victor Osimhen ya ƙara na uku na hudu.
A ɗaya wasan daf da ƙarshen kuma, Kamaru ce za ta fafata da Jamhuriyar Congo a ranar Alhamis, inda duk wanda ya yi nasara a ciki, zai fuskanci tawagar ta Nijeriya a ranar Lahadi mai zuwa.
Wasan na yau dai shi ne na farko tsakanin ƙasashen tun bayan shekarar 2005, lokacin da Nijeriya ta doke Gabon da ci 2-0.