Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Satar Mota A Gidan Gwamnatin Kano

Hukumomin tsaro a jihar Kano, sun samu nasarar kama wani mutum mai suna, Ya’u Inuwa dan Shekaru 50, bisa zarginsa da alaka da satar Mota a fadar gidan Gwamnatin Kano.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin sa na Facebook.

Sanarwar ta ce bayan samun labarin Sace motar, kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin toshe ko ina.

Binciken da jami’an yan sandan suka gudanar ne yakai ga Gano motar kirar Toyota Hilux, a unguwar Uku yan Awaki da aka samu labarin bacewar ta a ranar 11 ga watan Nuwamban 2025.

Wanda ake zargin yana daya daga cikin Direbobin fadar gwamnatin Kano, da ya hada kai da wasu mutane biyu da ake ruwan su yanzu.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano CSP ya ce mutumin da ake zargin yana tsare a wajen su kuma ya Amsa laifin tare da ci gaba da neman wadanda suka gudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *