Shugabannin Kungiyoyin NLC da TUC sun nuna ba za su goyi bayan karin farashin man fetur ba Ma’aikatan Najeriya sun ba Bola Tinubu shawara cewa gwamnatinsa ta gyara matatun danyen mai ‘Yan kwadago sun nuna ba za su yi na’am da janye tallafin fetur idan ba za a farfado da matatu ba:
Kungiyoyin NLC da TUC na ‘yan kwadago da ‘yan kasuwa a Najeriya, sun yi magana a kan batun janye tallafin man fetur da za ayi a bana. Punch ta rahoto kungiyoyin su na masu cewa za su goyi bayan dakatar da tallafin fetur ne idan gwamnatin Bola Tinubu za ta gyara matatun mai
Muddin ba za a farfado da matatun danyen mai da ake da su, sannan a kafa wasu kananu ba, kungiyoyin sun ce za su fito su shirya zanga-zanga.
Ministar tattalin arziki, tsare-tsare da kasafin kudi, Zainab Ahmed ta ce daga Mayun 2023, gwamnati ba tayi wani tanadi na rage farashin fetur ba.
A matsayinsa na ma’aji, da aka zanta da shi kwan nan, Kwamred Hakeem Ambali ya ce har gobe kungiyar NLC ba ta goyon bayan a janye tallafin.
Kamar yadda yake fada, ya zama dole gwamnati ta gyara matatun da ke tace danyen fetur, ya ce bai dace a rika shigo da mai daga kasashen ketare ba.
Haka zalika shugaban kungiyar malaman makaranta a Najeriya, Titus Amba ya nuna su na tare da uwar kungiyar kwadago dari bisa dari a kan batun.
Sai dai Asiwaju Bola Tinubu ya fada, kuma ya nanata cewa gwamnatinsa za ta cire tallafin man fetur da zarar ya shiga ofis. ‘Dan takaran shugaban kasan na APC a 2023 yana ganin talaka ba ya cin moriyar kudin tallafin da ake biya, ya ce masu kudi ne suke amfana da tsarin.