Home » Wata Cibiyar Tattara Zakka Ta Yi Nasarar Tara Naira Miliyan 90

Wata Cibiyar Tattara Zakka Ta Yi Nasarar Tara Naira Miliyan 90

by Anas Dansalma
0 comment

Wata cibiyar Tattara zakka da sadaƙa da ke Abuja da aka fi sani da NASFAT ta yi nasarar tattara kuɗi har naira miliyan casa’in a cikin shekaru huɗu.

Wannan jawabi ya fito ne daga bakin shugaban wannan cibiyar Alhaji Isiaq Ajibola, ya bayyana hakan, inda ya ƙara da cewa sun kuma yi nasarar tattara naira miliyan 500 a faɗin ƙasar nan.

An ƙafa cibiyar ne a Abuja a shekarar 2019.

Sannan Ajibola ya bayyana cewa cibiyar na amfani ne da kuɗaɗenta wajen taimakawa talakawa ta fuskar tallafi da taimako ta fannin ilimi da harkar lafiya.

 Ya kuma tabbatar da cewa cikin ayyukan da wannan cibiya ta yi, sun haɗa da siyo keke mai ƙafa uku, da kwamfutoci da injinan wanki da ma ƙarin wasu kayayyaki da suka suka raba a matsayin tallafi na jari ga masu buƙata.

Hakan dai na nuni da cewa kusan kaso 70 cikin 100 na kuɗaɗen da suka samu tare da raba su sun tafi ne a ɓangaren ba da jari ga al’umma a cewa shugaban.

Wannan dai ka iya zama ƙaimi ga sauran mawadata da ƙungiyoyin tatattara zakka kan ƙara dagewa wajen ganin an taimaka wa talakawa musamman a wannan wata na Ramadan.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?