Home » NLC Za Ta Yi Zanga-zanga Kan Ƙarancin Takardun Kuɗi a Najeriya

NLC Za Ta Yi Zanga-zanga Kan Ƙarancin Takardun Kuɗi a Najeriya

by Anas Dansalma
0 comment

Kungiyar kwadugo ta kasa tayi kira ga ma’aikata da su fita zanga-zanga daga ranar litinin mai zuwa saboda Ƙarancin Kuɗade a hannun al’umma.

 A Najeriya dai ana cigaba da fuskantar ƙarancin kuɗi a hannun jama’a wanda Hakan na zuwa ne tun bayan da Babban Bankin Kasa ya bada sanarwar canja fasalin kuɗi da kuma rage amfani da tsabar kuɗi a fadin kasar.

Lamarin bai yiwa ƴan ƙasa daɗi ba. Kuma tasa har kungiyoyin fafutuka suka soma tasowa domin ganin bankin yayi abinda ya dace akan lamarin.

Wannan ne dalilin da ya sa ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa ta yi kira ga duk ma’aikata da su  ɗaura ɗamara su dira a Ofishin babban banki na kowacce jiha dake ƙasar nan domin gudanar da zanga-zanga.

Hukumar ta ce, lamarin zai gudana ne daga sati mai kamawa idan har ba a samu chanji ba a kan ƙarancin kuɗin kashewa da ya addabi jama’a a ƙasa.

Shugaban na NLC, Joe Ajaero, ya ce umarnin ƙungiyar bai sauka akan kowane ma’aikaci ba, kuma ya zama dole saboda tun tuni suka bawa babban bankin sati ɗaya da ya warware matsalar amma lamarin ya ta’azzara.

Sakamakon ƙarewar lokacin, ya ce babu wani zaɓi face su ɗunguma shi da ƴaƴan ƙungiyar na kowacce jiha zuwa ofishin CBN na kowacce jiha domin sauya akalar mahukuntan bankunan a kan lamarin domin walwalar ƴan ƙasa.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi