Home » NNPP Ta Mai Da Martani Ga APC Kan Sake Nazarin Sakamakon Zaɓe

NNPP Ta Mai Da Martani Ga APC Kan Sake Nazarin Sakamakon Zaɓe

by Anas Dansalma
0 comment

Jam’iyyar NNPP a jihar Kano, ta mayar wa APC mai barin gado martani game da kiraye-kirayen da take yi cewa hukumar zabe ta sake nazari kan sakamakon zaɓen gwamnan jihar da ya bai wa Abba Kabir Yusuf nasara a zaben da aka yi  na gwamnoni.

APC  a jahar kano dai ta ce ba ta amince da sakamakon zaben ba, kuma za ta garzaya kotu don ƙalubalantar sa.

To, sai dai shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Umar Haruna Doguwa ya ce, duk masu bai wa Dr Nasiru Yusuf Gawuna shawarar ya je kotu to kuwa so suke ya yi biyu babu.

Ya kara da cewa,  indai kan batun garzayawa kotu ne,to la shakka basa jin komai, a shirye suke dasu amsa kiran kotun, tun da  sun tabbatar su na da gaskiya,domin kuwa  an yi sahihin zabe, dan haka ba za su hana kowa zuwa kotu ba.”

Abba Kabir Yusuf ya yi nasara a zaben gwamna da aka gudar a ranar 18 ga watan Maris 2023, inda ya kada abokin takararsa na jam’iyyar APC mai mulki kuma mataimakin gwamna Dr Nasiru Yusuf Gawuna.

Sai dai jam’iyyar APC ta ce za ta kalubalanci zaben, bi sa zargin an yi aringizon kuri’u a zabe

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi