Hukumar wayar da kan jama’a ta Najeriya, NOA, ta samu lambar yabo ta ƙwarewa a fannin wayar da kan jama’a da kuma karfafa kishin ƙasa.
Ƙungiyar ’Yan Jarida Mata ta Najeriya, NAWOJ, ce ta karrama hukumar a yayin taron Women in Security Summit 2026.
An bayar da wannan lambar yabo ga NOA ne bisa gagarumar gudunmawar da take bayarwa wajen wayar da kan al’umma, inganta isar da sako ga jama’a, da kuma dabbaka ɗabi’u nagari da ke ƙarfafa haɗin kan ’yan Najeriya.
Haka kuma, an yaba wa Darakta-Janar na hukumar, Malam Lanre Issa-Onilu, bisa jajircewarsa da salon jagorancinsa da kuma sauye-sauyen da yake aiwatarwa a cikin hukumar.
Hukumar NOA ta bayyana cewa wannan karramawa wata muhimmiyar shaida ce ta ƙoƙarin da ma’aikatanta ke yi wajen isar da saƙonnin wayar da kai da kuma fahimtar jama’a kan muhimman batutuwan ƙasa.
An bayyana lambar yabon a matsayin ƙarin ƙwarin gwiwa ga hukumar da ma’aikatanta domin ci gaba da ƙarfafa ayyukan wayar da kan jama’a da inganta kishin ƙasa a faɗin Najeriya.

