Rundunar Ƴan Sandan Jihar Sokoto ta ce ta yi nasarar daƙile hare-haren ƴanbindiga guda biyu a ƙananan hukumomin Shagari da Rabah, inda ta ƙwato dabbobi sama da 450 da maharan suka kwashe.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Ahmad Rufa’i, ya fitar, ya ce harin na farko ya faru ne da misalin ƙarfe 7:20 da yammacin ranar 4 ga Agusta, lokacin da ƴanbindiga ɗauke da makamai suka kai hari ƙauyukan Horo Birni da Marake a ƙaramar hukumar Shagari.
Sanarwar ta ce bayan samun kiran gaggawa, jami’an rundunar da sojoji suka iza zuwa wurin, inda suka yi musayar wuta da maharan.
Ya ce maharan sun tsere zuwa cikin daji bayan sun sha ƙarfinsu, tare da barin dabbobin da suka kwashe, waɗanda suka haɗa da shanu 195, tumaki 84 da raƙuma biyu.
Sai dai mutum biyu daga cikin mazauna yankin sun samu raunukan harbin bindiga, kuma an kai su asibiti domin samun kulawa.
A wani hari daban da ya faru da misalin ƙarfe 8:10 na dare a ƙauyen Maikujera da ke ƙaramar hukumar Rabah, ƴanbindiga sun sace dabbobi 171, da suka haɗa da raƙuma, shanu, tumaki da awaki.
Rundunar ta ce jami’anta sun tare hanyoyin fita daga ƙauyen tare da fafatawa da maharan, lamarin da ya tilasta musu tserewa tare da barin dukkan dabbobin da suka sace.

