Hukumar tsaron civil defense reshen jihar Jigawa, ta samu nasarar kama wasu daga cikin mutane da ake zargi da yin amfani da Adduna da Gatari wajen halaka wani jami’in hukumar mai suna Bashir Adamu Jibrin.
Kakakin hukumar tsaron Civl defense reshen jihar Jigawa, Badruddeen Tijjani Mahmud, ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce lamarin ya faru ne lokacin da jami’ansu suke gudanar da aiyukansu.
- Gwamnatin Kano Ta Karɓi Rahoton Binciken Kwamishinan Da Ake Zargi Da Belin Danwawu
- Makon Shayar Da onon Uwa Ta Duniya
A cewarsa wasu batagari ne suka yi amfani da Adduna da Gatari suka datsa kansa, a kasuwar Shuwarin dake jihar lokacin da sukaje don kama wasu da ake zargi da aikata laifuka.
Marigayin dan asalin jihar Kano, ne inda yanzu haka aka dawo da gawarsa zuwa ga danginsa don yi masa sutura kamar yadda addinin musulinci ya tanada.

