Kwamitin Zartaswa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar adawa ta PDP ya tabbatar da Umar Damagum a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa.
Wannan dai na zuwa ne a yayin zaman NEC na 102 da ke gudana a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja.
A jawabinsa na karɓar shugabanci, Damagum ya gode wa sauran mambobin Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) bisa taimako da haɗin kai da suka ba shi wajen gudanar da aikinsa.
- PDP Ta Miƙa Wa Kudancin Najeriya Takarar Shugaban Kasa A 2027
- PDP Ta Bugi Kirjin Cewa Ita Ce Za Ta Iya Dawo Da Najeriya Turba Mai Kyau.

