• Home  
  • Tinubu Ya Gana Da Shugaban Brazil Lula
- Babban Labari - Labarai

Tinubu Ya Gana Da Shugaban Brazil Lula

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gana da takwaransa na Brazil, Luiz Inacio Lula da Sailva a birnin Brasilia bayan shugaban na Najeriya ya isa ƙasar. Shugabannin biyu za su tattauna inganta haɗakar diflomasiyya da sauran abubuwan da suka ce zai amfani ƙasashen biyu. A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya Bayo Onanuga […]

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gana da takwaransa na Brazil, Luiz Inacio Lula da Sailva a birnin Brasilia bayan shugaban na Najeriya ya isa ƙasar.

Shugabannin biyu za su tattauna inganta haɗakar diflomasiyya da sauran abubuwan da suka ce zai amfani ƙasashen biyu.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya Bayo Onanuga ya fitar, ya ce akwai alaƙa mai kyau tsakanin Najeriya da Brazil, inda ya ce a watan Maris na 2025, ƙasashen biyu sun ƙulla yarjejeninyar inganta noma da kasuwanci da tsaro da makamashi da ilimi da ma’adinai.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000