• Home  
  • PDP Ta Bugi Kirjin Cewa Ita Ce Za Ta Iya Dawo Da Najeriya Turba Mai Kyau.
- Babban Labari - Labarai

PDP Ta Bugi Kirjin Cewa Ita Ce Za Ta Iya Dawo Da Najeriya Turba Mai Kyau.

Jam’iyyar PDP ta Najeriya ta ce babu gudu ba ja da baya kan shirye-shiryenta na gudanar da babban taronta wanda aka shirya yi a ranar 15 ga watan Nuwamban shekarar nan ta 2025 a jihar Oyo da ke kudancin Najeriya. PDP ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ƙungiyar gwamnoninta ta fitar bayan taron […]

Jam’iyyar PDP ta Najeriya ta ce babu gudu ba ja da baya kan shirye-shiryenta na gudanar da babban taronta wanda aka shirya yi a ranar 15 ga watan Nuwamban shekarar nan ta 2025 a jihar Oyo da ke kudancin Najeriya.

PDP ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ƙungiyar gwamnoninta ta fitar bayan taron gwamnonin da aka yir a jihar Zamfara a ranar Asabar 23 ga Agusta.

Gwamnonin sun yi kira ga mambobin jam’iyyar da su jajirce domin tabbatar da yiwuwar babban taron, domin a cewarsu PDP ce kaɗai jam’iyyar da za ta iya mayar da Najeriya turba mai kyau.

“Muna kira ga mambobinmu da su dage wajen yaƙi da masu shirya mana tuggu da zagon ƙasa domin hana faruwar babban taronmu mai zuwa.”

“Jam’iyyar ta yaba da ƙoƙarin jagororinta bisa jajircewar da suka nuna a lokacin da ake guguwar ficewa daga cikinta,” in ji sanarwar wadda gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammad ya sanya wa hannu, sannan ta ƙara da cewa tsaiko ne da ba zai dakushe karɓuwar jam’iyyar ba a wajen masu zaɓe.

Ƙungiyar ta kuma nanata ƙudurin da ta ce jam’iyyar na da shi na ceto ƴan Najeriya da ma ƙasar daga APC, “wadda matakanta suka jefa ƴan ƙasar cikin ƙuncin rayuwa.”

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai