• Home  
  • PDP tsagin Wike ta zaɓi sabbin shugabanninta
- Babban Labari

PDP tsagin Wike ta zaɓi sabbin shugabanninta

Jam’iyyar PDP tsagin Mininstan Abuja, Nyesom Wike ta zaɓi Abdulrahman Mohammed a matsayin sabon shugabanta na ƙasa yayin da Samuel Anyanwu ya samu matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa. Mohammed da Anyanwu sun samu kujerunsu ta hanyar masalaha, tare da sauran mambobin kwamitocin jam’iyyar ta ƙasa guda 19 a babban taron jam’iyyar na shekarar 2026 da […]

Jam’iyyar PDP tsagin Mininstan Abuja, Nyesom Wike ta zaɓi Abdulrahman Mohammed a matsayin sabon shugabanta na ƙasa yayin da Samuel Anyanwu ya samu matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa.

Mohammed da Anyanwu sun samu kujerunsu ta hanyar masalaha, tare da sauran mambobin kwamitocin jam’iyyar ta ƙasa guda 19 a babban taron jam’iyyar na shekarar 2026 da aka gudanar a babban filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja a ranar Lahadi.

Daga cikin manyan ‘yan jam’iyyar da suka halarci taron akwai tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido da tsohon shugaban Majalisar Dattijai, Bukola Saraki da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Ahmed Makarfi, da sauransu.

Wike, wanda aka bayyana a matsayin jagoran jam’iyyar ta ƙasa ya ce an fara warkar da PDP daga matsalolin da take fuskanta.

Ya tabbatar wa mambobi cewa PDP za ta shiga zaɓe a shekarar 2027.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai