A wani ci gaban kuma, dangane da alƙawuran da shugaban ƙasa, Tinubu ya yi, ya bayyanawa cewa zai sake duba maganar sauya fasalin kuɗin ƙasa da babban bankin ƙasa ya yi a watannin baya
Za a iya cewa ba wani sabon abu ba ne duba da alwashin da Tinubu ya ci na sake duba batun sauya fasalin kuɗi na naira, ganin cewa tun kafin ya ci zaɓe yake sukar lamarin.
Ga ci gaban labarin tare da Hassan Abdu Mai Blouse
Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa. Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.