Gwamnan jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya amince da nadin Alhaji Laminu Rabiu a matsayin sabon sakataren zartarwa na hukumar jin dadin alhazai ta jiha.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, da aka fitar a safiyar yau Talata.
Gwamnan ya kuma maye gurbin Sheikh Saleh Pakistan da Alhaji Yusuf Lawan a matsayin sabon shugaba.
Daga cikin wadanda aka nada a tsayin mambobin Sheik Abbas Abubakar Daneji, da Sheik Shehi Maihula, da Amb, Munir Lawan, da Sheik Isma’il Mangu da Hajia Aishatu Munir Matawalle da kuma Dr, Sani Ashir.
Sanarwar ta ce wadanda aka nada zasu karbi ragamar aikin hukumar nan take, domin ganin an samu nasarar gudanar da aikin hajjin bana.