Majalisar dinkin duniya ta ware ranar 20 ga watan Maris na kowacce shekara a matsayin ranar kula da lafiya da kuma tsaftar baki ta duniya.
An fara ayyana ranar kula da lafiyar baki da hakora ne a shekarar 2007 amma ba a fara bikin ranar ba sai a shekarar 2013..
An ware ranar ce don wayar da kan jama’a kan yadda za su kula da tsaftar bakinsu don guje wa cututtuka da ka iya shafar baki ko hakori.
Wasu yan Najeriya sun yi bayan irin hanyoyin da suke bi wajen kula da tsaftar bakinsu.
Marry tace idan ta tashi da safe abunda ta fara yi shine wake bakinta da man goje baki da buroshinta sannan tace ba iya hakoranta kawai take wankewa ba har da harshenta duk tana wakewa.
Haka shima Sadiq yace hanyoyi biyu ne ake wake baki akwai na zamani sannan akwai na gargajiya wanda aka saba tun asali wato yin amfani da gawayi da asuwaki. Duk yana iya amfanin dasu duk domin tsafatce bakinsa.
Ma’aikacin lafiya mai kula da tsaftar baki wato Kwararren likitan hakori Dr umar daga asibitin koyawa na malam Aminu kano .ya bayyana irin cututtukan hakori da aka fi cin karo da su musamman a Najeriya. Da karin bayani game da muhimmancin wannan rana.
Yace cutar ramin hakuri na daya daga cikin cututtukan da suka fi adabar al’ummar najeriya.
wanda dayawa daga cikin muatane suna ganin idan kasami cramin hakuri sai dai kawai acire maka hakorin wanda ba haka bane akwai abubuwa da dama akeyiwa hakori wanda ba sai an cire ba.
sannan akwai abubuwan ma da za’ayiwa mutun wanda bazata kawo ramin hakurin ba da sauran cututtuka na daddashi da harshe da sauransu.
haka kuma Dr umar yace rana ce mai muhimmanci a garesu wanda suke amfani da ita wajen fadakar da al’umma kan yadda zasu kula da lafiyar bakinsu wanda ya hada da ganda, daddashi, harshe, da hakora da duk abinda yake cikin baki.
sannan suna jadaddawa al’umma cewa kowani irin mutum yaro da babba ya kamata ace duk bayan wata shida yarika zuwa asibiti ana duba masa lafiyar hakorinsa da bada shawarwwri da zakabi domin kula da lafiyar hakoransa
Dr umar ya kara da bayyana wasu matsaloli da rashin kula da tsaftar baki da hakori ka iya haifar wa.
Rashin kula da tsaftar hakori daya daga cikin abubuwan da yake jawowa shine cutar daddashi, zakaji hakoranka na rawa yasa haka kawai hakora surika faduwa batare da ka tabasu ba.
Ranar dai wata dama ce ta zuwa asibitin hakori don a duba lafiyar hakoranmu kyauta.
Taken ranar na wannan shekarar shine tsaftacen baki shi ke kawo anashuwa.