• Home  
  • Majalisa Ta Amince Da Dakatar Da Fubara
- Babban Labari - Labarai - Siyasa

Majalisa Ta Amince Da Dakatar Da Fubara

Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da dokar ta baci, da kuma dakatarwar da shugaba Tinubu ya yi wa gwamanan jihar Ribas Siminalayi Fubara cikin yanayi na kusan na bai daya.

Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da dokar ta baci, da kuma dakatarwar da shugaba Tinubu ya yi wa gwamanan jihar Ribas Siminalayi Fubara cikin yanayi na kusan na bai daya.

Wannan ya gudana ne da ranar Alhamis 20/Maris/2025 yayin zaman majalisar, karkashin jagorancin Honarabul Tajuddin Abbas.

Sai dai tuni masana masu sharhi akan dokoki suka far yin tir da abin da ya faru, inda sananne daga cikin ‘yan rajin kare hakkin bil Adama a Najeriya Barr Abba Hikima ya bayyana hakan a matsayin rashin kasar ma baki daya in da ya ce “Ba kasa fa jama’a”.

Tuni dai rahotanni suka tabbatar da cewa sojoji sun karbe ikon gudanarwa a jihar Ribas, inda za su kwashe watanni shida suna gudanar da harkokin jihar kamar yadda shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ayyana.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai