Kasar Burtaniya ta bayyana damuwarta kan tabarbarewar tsaro a Najeriya, inda ta bayyana hakan a matsayin “babban abin tada hankali” da ke faruwa sakamon rikice-rikicen da suka ki ci-suka ki cinye wa a jamhuriya Nijar da kuma Kasar Sudan.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula sakamakon hare-haren ‘yan bindiga ke kai wa a Filato, Binuwai, da Jihar Borno.
Babban kwamishinan Burtaniya a Najeriya, Richard Montgomery ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a gidansa da ke Abuja a ranar Larabar gabata.
- Kungiyar Gauta Club Ta Goyi Bayan Shugabannin Kafafen Yada Labarai Kan Dakatar Da Shirin Siyasa Kai Tsaye
- An Rufe Dakunan Kwanan Dalibai A Jami’ar Maryam Abacha Kano
Mista Richard ya danganta abin da ke faruwa da rashin zaman lafiyar da ake fama da shi a wasu kasashe dake makwabta da Najeriya kamar janhuriya Nijar da kuma kasar Sudan.
Ya kara da cewa gwamnatin Burtaniya na kokarin binciken hakikanin abin da ke janyo wannan matsalar domin kawo karshen ta, ta hanyar wani aiki na hadin guiwa da ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro.

