Rikicin manoma da makiyaya, a jihar Jigawa yayi sanadiyar mutuwar mutum daya da jikkata mutane biyu, a kauyen Yelwa-Musari dake gundumar Kadara karamar hukumar Guri ta jihar.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Jigawa, SP Shiisu lawan Adamu, ne ya tabbatar da faruwar lamarin.
Rundunar yan sandan ta ce baya ga mutum daya da ya rasa ransa da kuma wadanda suka jikkata akwai kuma mutum daya da ba a gona inda yake ba har zuwa yanzu.
SP Shiisu Lawan, ya kara da cewa, tuni aka tura dakarun yan sanda don wanzar da zaman lafiya a yankin kuma al’amura sun koma daidai.
Sai dai rundunar yan sandan jihar Jigawan bata yi cikakken bayani ba, kan yawan mutane data kama da ake zargi da hannu kan faruwar lamarin.
Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa ricikin ya fara tun a ranar Asabar da Lahadi, inda aka kone gidaje da dama.

