• Home  
  • Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ƙara tsaurara tsaro a bikin Easter.
- Babban Labari

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ƙara tsaurara tsaro a bikin Easter.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin kwamishinanta, CP Ibrahim Adamu Bakori, ta taya Kiristoci murnar bikin Easter tare da tabbatar da cewa an tanadi isasshen tsaro a duk faɗin jihar. Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa […]

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin kwamishinanta, CP Ibrahim Adamu Bakori, ta taya Kiristoci murnar bikin Easter tare da tabbatar da cewa an tanadi isasshen tsaro a duk faɗin jihar.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Asabar.

Sanarwar ta ce, an tura jami’an ƴan sandan  zuwa wuraren ibada da sauran muhimman wurare domin tabbatar da tsaro da  zaman lafiya yayin gudanar da bikin.

Haka zalika, an umurci shugabannin sassan rundunar da suka hada da kwamandodjin ƴan sanda da baturan ƴan sanda su ƙara tsaurara matakan tsaro da sanya ido.

A ƙarshe rundunar ta buƙaci jama’a a duk lokacin da suka ga wani abu da amince dashi ba, su gaggauta sanarwa a ofishin ƴan sanda mafi.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000