• Home  
  • Rundunar ƴan sandan jihar Gombe ta dawo da dokar taƙaita zirga-zirgar babura.
- Babban Labari

Rundunar ƴan sandan jihar Gombe ta dawo da dokar taƙaita zirga-zirgar babura.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta sake dawo da dokar takaita zirga-zirgar babura a cikin birnin Gombe, a wani mataki na ƙara tsaurara tsaro da daƙile ayyukan masu aikata laifuka. Dokar, wadda ta haramta amfani da babura daga karfe 7:00 na yamma zuwa 6:00 na safe kowace rana, za ta fara aiki daga ranar Juma’a, […]

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta sake dawo da dokar takaita zirga-zirgar babura a cikin birnin Gombe, a wani mataki na ƙara tsaurara tsaro da daƙile ayyukan masu aikata laifuka.

Dokar, wadda ta haramta amfani da babura daga karfe 7:00 na yamma zuwa 6:00 na safe kowace rana, za ta fara aiki daga ranar Juma’a, 3 ga Afrilu, 2026.

Wannan mataki na zuwa ne bayan wani muhimmin taron tsaro da ya haɗa jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki, inda aka yi nazari kan halin tsaro a jihar tare da duba hanyoyin da za a ƙara inganta tsaro.

A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya fitar, ya bayyana cewa an cimma matsayar ci gaba da wannan doka ne bayan tattaunawa mai zurfi da kuma la’akari da yadda ake amfani da babura wajen aikata miyagun laifuka, musamman da daddare.

Rundunar ta ce matakin na daga cikin dabarun da ake amfani da su domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da tabbatar da zaman lafiya a faɗin birnin.

Ta kuma yi kira ga mazauna jihar da su bi dokar tare da bai wa jami’an tsaro haɗin kai, tana mai jaddada muhimmancin sa ido da kai rahoton duk wani motsi ko abu da ke tayar da hankali ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.

Rundunar ’yan sandan ta sake tabbatar da ƙudirinta na ci gaba da tsare lafiyar al’umma, tare da alƙawarin sanar da jama’a duk wani sabon ci-gaba game da halin tsaro a jihar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai