Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta sanar da dakatar da wasannin tashe watan Azumi wanda aka fi a cikin ƙwayar birnin kano.
Wannan umarni ya fito ne ta bakin kakakin rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya sanar da hakan.
A cewarsa, dalilin haramta wasan tashen shi ne akan samu wasu da kai yi basaja a matsayin masu tashen wajen aiwatar da mugayen laifuka kamar ƙwacen wayar hannu da shan miyagun ƙwayoyi da makamantansu.
Inda ya tabbatar da cewa; duk wanda aka kama da saɓawa wannan doka, to tabbas doka za ta yi aiki a kansa.
Sannan hukumar ‘yan sandan ta ƙara tabbatar da hana dokar kilisa ba tare da bin ƙa’idar da aka tanada ko kunna abubuwan fashewa da aka fi sani da Knock-out.
Su ma ya tabbatar da cewa duk wanda aka kama da wannan laifi to zai ɗanɗana kuɗarsa.