sabon zaɓaɓɓen mataimakin shugaban ƙasar Najeriya Sanata Kashim Shettima ya kai wa tsofaffin shugabannin Najeriya Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Abdulsalami Abubakar ziyara a Minna, babban birnin jihar Neja.
Shettima ya kwatanta tsoffin shugabannin a matsayin mutanen masu dattaku da kuma ubannin ƙasa, inda ya ce gwamnati mai zuwa za ta yi aiki da su domin ciyar da ƙasar gaba.
Kashim yace zasu ci gaba da tuntuɓarsu a kowane lokaci domin samun shawarwari kan hanyoyin da za a bi wajen magance matsaloli da ƙasa ke fuskanta.
Daga bisani kuma ya jagoranci tawagarsa wajen kai gaisuwa ga Sarkin Minna Dakta Umar Farouq Bahago, inda aka yi addu’o’i don samun zaman lafiyar ƙasa.