Karamin ministan albarkatun man fetur na Najeriya Timipre Sylva ya yi murabus daga mukaminsa domin neman sabon wa’adi a matsayin gwamnan jihar Bayelsa mai arzikin man fetur a yankin Neja Delta.
Wasu majiyoyi a ma’aikatarsa da suka bukaci a sakaya sunansu ne suka shaida wa majiyarmu a jiya.
Murabus din Sylva na zuwa ne kwanaki 60 kacal, kafin wa’adinsa a kan mukamin karamin ministan albarkatun mai ya kare kuma a daidai lokacin da ake shirin kafa sabuwar gwamnati a Najeriya,
Rahotanni sun tabbatar da cewa, ministan ya mika wa shugaba Buhari kuma babban ministan albarkatun man fetur takardar murabus dinsa tun a makon da ya gabata, kuma tuni ya daina zuwa ofishinsa, a cewar wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta.
Haka kuma, wata majiya tabbatar da cewa ƙaramin ministan na neman tikitin takarar gwamnan jihar Bayelsa a ƙarkashin inuwar jam’iyyar APC mai mulki a zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka shirya gudanarwa a ranar 14 ga watan Afrilun mai zuwa.
A watan Agustan shekarar 2019 ne aka nada Sylva a matsayin karamin ministan albarkatun man fetur, inda ya jagoranci manyan sauye-sauye a fannin mai wadanda suka hada da zartar da dokokin da suka yi wa tsarin kasafin kudin sashen kwaskwarima a wani yunkuri na karfafa masu zuba hannun jari guiwa.