An bayyana rashin haɗin kai tsakanin al’ummar arewacin Nijeriya amatsayin abin da ke ƙara janyo wa yankin koma baya ta fuskar ci gaba da kuma rusa zamankewarsu. Dattijo a arewacin Nijeriya kuma ɗan kasuwa, Alhaji Shehu Ashaka, ne ya bayyana hakan yayin da yake tattaunawa da gidan telebijin da Radiyo na Muhasa.
Alhaji Shehu Ashaka, wanda haifanfan jihar Kano ne, daga arewacin Nijeriya, ya ce wannan matasalar ta faro ne sakamakon sakin kyawawan ɗabi’u da shugabannin baya suka ɗora jama’a akai.‘’duk wani abu daka sani shugabannin mu sun taho dashi na son juna da ƙaunar juna da yan uwantaka ana tafiya kaɗan-kaɗan ana yarwa har yanzu an kusa yarwa ya zama babu komai a wajen mu ƴan Arewa’’.
Ya ƙara da cewa tsoron da ake yiwa al’ummar yankin da kuma addininsu da siyasar su, su da kansu suke zubar da ita har ta kusa ƙarewa, saboda ƙiyayya da hassada ta ƙin juna.
Sai dai ya ce har yanzu ba a makara ba, domin al’ummar arewacin Nijeiya sun san ba akan daidai ake tafiya ba, tunda yawancin matsalolin da yankin yake fuskanta ba yau aka fara shi ba.
‘’ Na yi irin waɗannan maganganun da yawa, domin na taɓa faɗawa tsohon shugaban Nijeriya, Marigayi Muhammadu Buhari, cewa in kayarda ka tafi ka barmu baka ,kashe wannan wutar da ake ciki ba, a arewa babu mai kashe mana ita har yanzu bata mutu ba domin waɗanda suke cikin gwamnatin a suma a firgice suke.
A ƙarshe ya ce sai ƴan arewa sun dage da yin addu’a da neman gafarar Allah, da irin abubuwan da ake yi na ba daidai ba, a dawo, a soma gyarawa za a samu mafita amma matuƙar aka ci gaba da tafiya akan ci gaban mai haƙan Rijiya ba za a ci gaba ba.
