• Home  
  • Sarkin Ibadan Ya Rasu Yayin Da Ake Shirin Bikin Cikarsa Shekara Guda A Mulki
- Babban Labari - Labarai

Sarkin Ibadan Ya Rasu Yayin Da Ake Shirin Bikin Cikarsa Shekara Guda A Mulki

Allah Ya yi wa Sarkin Ibadan (Olubadan), Oba Owolabi Olakulehin, rasuwa a yayin da ake shirye-shiryen bukukuwan cikarsa shekara guda a bisa karagar mulki. Shaidu sun bayyana cewa Oba Owolabi Olakulehin ya koma ga Mahaliccinsa ne a safiyar ranar Litinin ɗin, 7 ga watan Yuli, 2025. Ya rasu ne kwana uku bayan kammala bikin cikarsa […]

Allah Ya yi wa Sarkin Ibadan (Olubadan), Oba Owolabi Olakulehin, rasuwa a yayin da ake shirye-shiryen bukukuwan cikarsa shekara guda a bisa karagar mulki.

Shaidu sun bayyana cewa Oba Owolabi Olakulehin ya koma ga Mahaliccinsa ne a safiyar ranar Litinin ɗin, 7 ga watan Yuli, 2025.

Ya rasu ne kwana uku bayan kammala bikin cikarsa shekara 90 a duniya.

Oba Oluwabi, wand aka haifa a shekarar 1935, ya hau karagar mulki ne a watan Yulin shekarar 2024, inda ya gaji mariya Oba Lekan Balogun.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai