Gwamnatin Sokoto Ta Ce Ba Zata Yi Sulhu Da Turji Ba Har Sai Ya Sako Mutanen Da Ya Sace

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ƙalubalanci jagoran ’yan bindiga Bello Turji, wanda ke neman sulhu, da cewa idan da gaske yake yi, to ya sako duk mutanen da ya yi garkuwa da su, ya daina kai hare-hare, kafin ta zauna da shi.

Mashawarci na musamman ga gwamnan Sakkwato a kan sha’anin tsaro, Kanar Ahmed Usman ne ya bayyana hakan baya yaɗuwar wani bidiyo da Turji ya saki, wanda a ciki yake neman a yi tsakaninsa da gwamnati.

Ɗan ta’addan wanda ya addabi yankunan jihar da makwabta ya saki bidiyon ne kwanaki kaɗan bayan jami’an tsaro sun kashe wasu gaggan kwamandojinsa da Faransa sama da 100.

Kamar Ahmed, a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa babu yadda za a tabbatar cewa neman sulhun Turji ba ta fatar baki ba ne, sai idan ya dakatar da kai wa al’ummo hare-hare saki duk mutanen da ya sace ba tare da ɓata lokaci ba.

“Idan har da gaske yana neman sulhu, to sai ya nuna a aikace, ya dakatar da hare-hare kan ƙauyuka tare da sakin duk mutanen da ke hannunsa ba tare da sharaɗi ba,” in ji Kanar Ahmed, wanda ke jaddada muhimmancin tsaron rayuka da lafiyar da kuma dukiyoyin al’umma ga gwamnatin Jihar Sakkwato.

Don haka ya, “Ba za a iya yin wata sahihiyar tattaunawar sulhu da za a yi a samu a yayin al’ummomi suke zaune cikin tsoro kuma ’yan ta’adda suke yin garkuwa da mutane.

“Matakin farko na samun zaman lafiya shi ne gina yarda ta hanyar ɗaukar ƙwararan matakai a aikace,” in ji jami’in gwmanatin.

Ya jaddada aniyar gwamnatin ga tabbatar da tsaro da zaman lafiya, amma ba za ta lamunci ta’addancibda sauran miyagun laifuka ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *