• Home  
  • Sarkin Yaƙin Masarautar Zazzau Ya Rasu Ana Tsaka Da Taro
- Babban Labari - Labarai

Sarkin Yaƙin Masarautar Zazzau Ya Rasu Ana Tsaka Da Taro

Masarautar Zazzau ta sanar da rasuwar ɗaya daga cikin manyan fadawan Sarkin Zazzau, kuma Sarkin Yaƙin Zazzau, Alhaji Rilwanu Yahaya Pate, da safiyar ranar Alhamis yayin da ake tsaka da taro a Babban Asibitin Gambo Sawaba da ke Kofar Gayan, Zariya. Marigayin yana cikin tawagar Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, lokacin da mutuwa ta […]

Masarautar Zazzau ta sanar da rasuwar ɗaya daga cikin manyan fadawan Sarkin Zazzau, kuma Sarkin Yaƙin Zazzau, Alhaji Rilwanu Yahaya Pate, da safiyar ranar Alhamis yayin da ake tsaka da taro a Babban Asibitin Gambo Sawaba da ke Kofar Gayan, Zariya.

Marigayin yana cikin tawagar Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, lokacin da mutuwa ta riske a wajen taron da kwamitin abokai na asibitin ya shirya.

Da yammacin ranar Alhamis, aka yi jana’izarsa a gidansa da ke Rimin Doko, a Unguwar Kaura, a cikin Birnin Zariya.

Babban Limamin Zazzau, Malam Dalhatu Kasim Imam ne, ya jagoranci sallar jana’izar da aka yi da misalin ƙarfe 5 na yamma.

Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, tsofaffin gwamnonin Jihar Kaduna, Alhaji Ahmad Makarfi da Alhaji Muktar Ramadan Yero, da kuma sauran al’umma ne suka halarci jana’izar.

A saƙon ta’aziyyarsa, Sarkin Zazzau ya jajanta wa iyalan mamacin da ɗaukacin masarautar bisa wannan babban rashi.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000