Daga: Safiyanu Haruna Kutama Da Abubakar Andulkadir Kurawa
Gwamnatin Tarayya Ta Ware Biliyan 252 Don Kammala Aikin Titin Abuja-Kaduna-Kano
Gwamatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ta ware wannan kudaden ne a yayin zaman majalisar zartarwa da ya gudana a jiya Litinin 3 ga watan Fabrairu a fadar shugaban kasar.
Haka kuma, FEC ta amince da karasa aikin hanyar zuwa matakai biyu don samar da ingantaccen aiki akan lokaci
A yayinda yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron, Ministan ayyuka David Umahi ya bayyana cewa sashe na farko zai tashi daga kan iyakar babban birnin tarayya Abuja zuwa jihar Neja, wanda aka ƙara wa kilomita 5.71 kan ainahin taswirar aikin na farko inda sashe na biyu ya sami karin yankuna a cikin jihar Kano, wanda ke da tsawon kilomita 17.
Umahi ya bayyana cewa a yayin gudanar da manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa masu zuwa, irin su manyan titin Lokoja-Benin da Abuja-Kano, za su yi amfani da ingantattun kwalta maimakon wanda aka saba gani a kullum da ke saurin fashewa
Ministan ya ƙara da cewa, ” a wannan karon ba zamu lamunci jan-ƙafa ko wani uziri irin na yin amfani da kayan aikin da zafin rana ka iya yi wa lahani ba, maimakon haka za mu gyara wuraren da suka lalace a baya kana mu tsaurara sanya ido sosai akan aikin.”
Gwamatin ta kuma amince da ware wani kasafin na Naira Bilyan 18 don sake gina hanyar Wusasa zuwa Jos dake jihar Kaduna.