• Home  
  • Tinubu ya umarci ICPC ta yi bincike kan kafa hukumar bogi
- Babban Labari

Tinubu ya umarci ICPC ta yi bincike kan kafa hukumar bogi

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ta gudanar da bincike kan wata hukuma ta bogi da ake zargin an ƙirƙire ta ba tare da sahalewar fadar shugaban ƙasar ba. A cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar, shugaban ƙasar ya umarci […]

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ta gudanar da bincike kan wata hukuma ta bogi da ake zargin an ƙirƙire ta ba tare da sahalewar fadar shugaban ƙasar ba.

A cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar, shugaban ƙasar ya umarci ICPC ta kammala binciken tare da gabatar masa da rahoto cikin kwanaki 30.

Sanarwar ta ce umarnin ya biyo bayan gano cewa majalisar bai wa shugaban shawara kan tattalin arziki da zuba jari daga ƙasashen ƙetare (PFIPC) hukuma ce ta bogi da ba a taɓa kafa ta ba.

Gwamnatin ta ce mutumin da take zargi mai suna Adeniyi Adeyemi Matthew ya riƙa bayyana kansa a matsayin Darakta Janar na hukumar, yana kuma iƙirarin cewa shugaban ƙasa ne ya naɗa shi.

Sanarwar ta ce binciken zai mayar da hankali kan zargin ƙirƙirar takardun naɗi da sauran takardun gwamnati na bogi, da kuma amfani da sunan shugaban ƙasa wajen neman ganawa da hukumomi da tattaunawar diflomasiyya.

Haka kuma ICPC za ta binciki zargin buɗe asusun banki na CBN da sahalewar wasu hukumomin gwamnati ta hanyar amfani da takardun da ake zargin na bogi ne.

“Dole ne a kare martabar fadar shugaban ƙasa da cibiyoyin gwamnatin tarayya daga masu yin sojan gona, masu ƙirƙirar takardu na bogi da masu amfani da sunan gwamnati ba bisa ƙa’ida ba,” in ji sanarwar.

Gwamnatin ta ƙara da cewa duk wanda bincike ya nuna yana da hannu a lamarin, za a hukunta shi bisa tanadin doka.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000