• Home  
  • Senegal: Jagoran ‘Yan Adawa, Ousmane Sonko, ya umarci magoyan bayansa su fito zanga-zanga
- Kasashen Ketare - Labarai

Senegal: Jagoran ‘Yan Adawa, Ousmane Sonko, ya umarci magoyan bayansa su fito zanga-zanga

Jagoran ‘yan adawa a Senegal, Ousmane Sonko ya buƙaci ‘yan kasa su fito kwansu da kwarkwata sun yi zanga-zangar adawa da manufar shugaba Macky Sall ta neman takara a karo na uku.

Senegal: Jagoran 'Yan Adawa, Ousmane Sonko, ya umarci magoyan bayansa su fito zanga-zanga

Jagoran ‘yan adawa a Senegal, Ousmane Sonko ya buƙaci ‘yan kasa su fito kwansu da kwarkwata sun yi zanga-zangar adawa da manufar shugaba Macky Sall ta neman takara a karo na uku.

A yau Litinin ake sa ran shugaba Sall zai gabatar da jawabi domin sanar da anniyarsa ta takara a zaben 2024 ko akasin haka- matakin da akasari kwararu a fannin shari’a ke cewa zai karya ƙundin tsarin mulkin Senegal.

Mista Sanko ya ce ya shafe tsawon shekaru yana fuskantar barazana a rayuwarsa, saboda kwadayin mulki na mutum guda.

A watan da ya gabata, Dubban mutane suka fantsama kan tituna su na zanga-zanga a biranen Senegal bayan yanke hukunci shekaru biyu kan Mista Sonko akan ɓata matasa.

Magoya-bayan Mista Sonko da wasu masu sharhi na ganin wannan hukuncin ƙoƙari ne kawai na datse shi daga takarar shugaban kasa a zaben baɗi.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000